Tinubu ya naɗa Sa’ad Namdas a matsayin daraktan BCDA, Obahiaghon da Umeoji a manyan muƙaman NDPHC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa tsohon Mia magana da yawun Majalisar Wakilai, Abdulrazak Sa’ad Namdas a matsayin sabon darakta janar na Hukumar Raya Yankunan Iyakokin Nijeriya (BCDA).

Wannan na nufin Dakta Namdas ya maye gurbin Dakta Dakorinama Alabo George, wanda ya yi murabus domin neman wani muƙamin siyasa a jiharsa.

Namdas tsohon ɗan Majalisar Wakilai ne da ya wakilci mazaɓar Ganye/Jada/Mayo Belwa/Toungo ta Jihar Adamawa, sannan ya yi takarar neman tikitin gwamna a zaɓen fidda gwani da aka kammala kwanan nan a jihar.

A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida kuma masani a harkokin hulɗa da jama’a, Namdas ya kuma taɓa zama Babban Sakataren Yaɗa Labarai na tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Boni Haruna.

Kazalika, Shugaba Tinubu ya naɗa Hon. Patrick Obahiagbon a matsayin Daraktan Zartarwa mai kula da Tsare-tsare da Harkokin Kasuwanci na Kamfanin Niger Delta Power Holding Company (NDPHC).

Shugaba Tinubu ya kuma sake naɗa Mista Chukwuma Umeoji a matsayin Daraktan Zartarwa mai kula da Harkokin Gudanarwa (Corporate Services) na NDPHC.

Obahiagbon ya maye gurbin Injiniya Omoregie Ogbeide-Ihama, wanda ya yi murabus daga muƙaminsa domin neman wata muƙamin siyasa a jiharsa. Obahiagbon ya taɓa zama ɗan Majalisar Dokokin Jihar Edo da kuma ɗan Majalisar Tarayya.

Shi kuma Mista Umeoji, tsohon ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Aguata ta Jihar Anambra, an sake naɗa shi bayan ya yi murabus domin neman wata muƙamin siyasa a jiharsa.

A cewar Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga, waɗannan naɗe-naɗe za su fara aiki ne a nan take, kamar yadda ya bayyana a wata takarda.

By Babaji