
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta bayyana cewa har yanzu ba ta karɓi ainihin kwafin hukuncin Kotun Tarayya da ke Lokoja wanda ya soke umarnin rajistar jam’iyyar NDC ba da aka yi a kwanan nan.
Kakakin shugaban INEC, Adedayo Oketola, ya ce hukumar ta samu rahotannin hukuncin da aka yanke a ranar 26 ga Yuni, 2026, amma ba za ta iya yin cikakken bayani kan hukuncin ba sai bayan ta samu kwafin hukuncin.
A cewarsa, sashen shari’a na INEC zai nazarci hukuncin da zarar an karɓi kwafin sannan hukumar ta yanke matakin da ya dace bisa doka.
A ranar Juma’a ne babbar kotun tarayya da ke Lokoja ta soke hukuncin da ta yanke a watan Disambar 2025 wanda ya umarci INEC ta yi wa jam’iyyar NDC rajista.
Sai dai shugaban NDC, Sanata Moses Cleopas, ya ce ba a soke rajistar jam’iyyar ba, yana mai bayyana cewa za su ɗaukaka ƙara zuwa kotun ɗaukaka ƙara.
Hukuncin ya janyo martani daga wasu jagororin adawa ciki har da Peter Obi da Sanata Henry Dickson, waɗanda suka bayyana matakin a matsayin barazana ga tsarin jam’iyyu da dama a ƙasar.
