
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gabriel Martinelli ya zura ƙwallo a raga a minti na 95, wanda hakan ya ba Brazil nasarar doke Japan da ci 2 da 1 a wasansu na zagayen ‘yan 32 na gasar Kofin Duniya da ke cigaba da gudana a Nahiyar Amurka.
Wannan al’amari ya sa Japan ta rasa damar tsallakewa zuwa zagaye na gaba duk da cewa ita ta fara zura ƙwallo a ragar Brazil a zangon farko na wasan ta ɗan wasa Kaishu Sano.
Bayan minti goma da fara zangon na biyu ne ɗan wasa Casemiro ya farke wa Brazil a lokacin da Gabriel ya jefa masa ƙwallo daga bugun tazara.
Brazil, wadda ta lashe gasar har sau biyar a tarihi, ta samu zura ƙwallo na biyu ne ta hannu Martinelli yayin da ake dab da ƙarƙare wasan, lamarin da ya jefa ta zagayen ‘yan 16.
