2027: INEC ta ba APC, PDP ADC, NDC da wasu jam’iyyu damar ɗora sunayen ‘yan takararsu a shafinta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta ba jam’iyyar APC da wasu jam’iyyun siyasa lambobin damar shiga tsarin ɗora sunayen ‘yan takara a shafinta na yanar gizo domin shirye-shiryen babban zaɓen 2027.

Rahotanni sun bayyana cewa, jam’iyyun da suka samu damar sun haɗa da APC, PDP, ADC, da kuma NDC da wasu jam’iyyu da nufin ba su damar gabatar da sunayen ‘yan takararsu a tsarin na INEC cikin wa’adin da hukumar ta gindaya.

Bayan kammala ɗora sunayen, ‘yan takarar za su fafata ne domin neman kujerun a shugaban ƙasa, Majalisar Dattawa, Majalisar Wakilai da kuma gwamnoni a mafi yawan jihohin ƙasar.

Sai dai jihohin Kogi da Osun ba sa cikin wannan jadawalin saboda suna gudanar da zaɓen gwamnoni a lokutan da suka bambanta da babban zaɓe.

Wani babban jami’in INEC ya tabbatar cewa jam’iyyar NDC na cikin jam’iyyun da aka bai wa damar shiga tsarin loda sunayen ‘yan takara.

Haka kuma ya musanta rahotannin da ke cewa an hana jam’iyyar samun lambar shiga tsarin, yana mai cewa an ba ta damar ci gaba da gudanar da aikin kamar sauran jam’iyyun da suka cancanta.

By Babaji