Kano: Samar da jari ne ginshiƙin bunƙasa kasuwanci, inji Shugaban ‘yan kasuwa a Bichi

Spread the love

Ƙungiyar ‘Yan kasuwar Zamani ta Bichi Traders Multi-Purpose Cooperative Society Limited, ta yi kira ga gwamnati, shugabanni, masu ruwa da tsaki, manyan ‘yan kasuwa da masu zuba jari da su haɗa hannu wajen bunƙasa harkokin kasuwanci a Ƙaramar Hukumar Bichi.

Shugaban Ƙungiyar ‘Yan kasuwar Zamani ta Bichin, Alhaji Abubakar Mazahimu Sale ne ya bayyana wannan kiran, bayan kammala gina kasuwar Kabiru Abubakar Ultra-Modern Market Bichi, ƙarkashin jagorancin Ɗanmajalisar Tarayya mai wakiltar Bichi, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar.

Ya ce, a wannan karon da ake shirin fara amfani da rukuni na biyu na shagunan da aka kammala, lokaci ne da yakamata shugabanni da masu ruwa da tsaki su ƙara himma wajen tabbatar da cigaban wannan babbar kasuwa da ɗanmajalisar ya zamanantar domin gogayya da manyan kasuwannin ƙasar Nijeriya dama wasu ƙasashen Afrika baki ɗaya.

Kazalika, Shugaban Ƙungiyar ‘Yankasuwar, ya shaida hakan zai samu ne ta hanyar samar da jari ga ‘yankasuwa tare da jawo manyan kamfanoni.

“Kasancewar a kasuwar muna da masu sana’oi kala daban-daban, sai muka kasa su kashi-kashi. Ma’ana ba da tallafin zai ƙunshi; masu furobishan, abinci, lemuka, na cikin kasuwar da ma sauran kasuwannin da suke cikin ƙwaryar Ƙaramar Hukumar Bichi. Waɗannan rukuni su muka fara ɗauka muka tantance su mun raba su zuwa ƙananun ‘yankasuwa da ‘yantsakiya da kuma manyan ‘yankasuwa.

Idan aka kammala da su kuma sai a ɗauki masu sana’ar kayan awo, kana masu sayar da yadiddika da atamfofi, sannan masu sai da takalma da mai. Haka dai za a bi masu sana’oin ɗaya bayan ɗaya, idan an kammala da wannan ɓangare a ɗauki wani ɓangaren na masu sana’a ta gaba, wannan shi ne tsare-tsaren da muka yi a yanzu, wanda tuni muka mika wa Kwamitin Kasuwanci na Ɗanmajalisar Tarayya mai wakiltar Bichi ta hannun Malam Zaharadden Bello da kuma Sakataren Kwamitin Bello Gadanya.” Alhaji Abubakar Mahimu Sale.

A hannu guda kuma, Ƙungiyar Kasuwar Zamanin ta yaba tare da jinjina wa Shugaban Majalisar ƙaramar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, bisa ƙoƙarin da yake yi na gayyato manyan ‘yan kasuwa daga Singa, da kuma manyan kamfanoni daga Kantin Kwari, waɗanda tuni suka kama wuraren haya domin fara sauke kayayyaki a kasuwar.

Haka kuma sun yaba wa Shugaban Kasuwar Zamanin, Alhaji Garba Tukur, tare da Shugaban Kwamitin Kasuwanci da Masana’antu na Ofishin Ɗanmajalisar Tarayya, SLA Zaharaddeen Bello, da kuma Malam Bello Gadanya, bisa kyakkyawar haɗin gwiwar da suke yi tare domin bunƙasa harkokin kasuwanci da cigaban kasuwar Kabiru Abubakar Ultra-Modern Market Bichi.

By Babaji

Leave a Reply