
A ranar Talata Kotun Ƙolin Amurka ta yi watsi da buƙatar Shugaba Donald Trump na ƙasar ta yunƙurin neman a taƙaice bayar da shaidar zama ɗan ta hanyar haifar mutum a ƙasar, hukuncin da ya jaddada ‘yancin zama ɗan ƙasa ga duk wanda aka haifa a Amurka.
A cewar Kotun, duk wanda aka haifa a Amurka na da damar mallakar shaidar zama ɗan ƙasa.
A shekarar da ta gabata ne Trump ya rattaɓa hannu akan wata doka da ke neman haramta wa yaran da aka haifa a ƙasar waɗanda iyayensu ke zama a Washington ba bisa ƙa’ida ba, ko kuma suka mallaki biza ta wucin gadi mallakar takardun zama ‘yan ƙasa.
Kotunan baya sun dakatar da matakin shugaban ƙasar, inda su ka ce dokokin zama ɗan ƙasa da ke ƙunshe cikin kundin tsarin mulkin ƙasar bai haramta hakan ba.
Kotun, wadda Mai Shari’a John Roberts da ƙarin wasu alƙalai suka jagoranci zamanta, sun yi watsi da buƙatar ta Trump.
Yunƙurin Trump na kawo ƙarshen wannan doka game da zama ɗan ƙasar Amurka, wani ɓangare ne na shirinsa na daƙile kwararar baƙi cikin ƙasar, wanda ya ƙunshi korar miliyoyin ‘yan ci rani da ba su da takardu tare da cire kariyar ‘yan wasu ƙasashe da dama.
