
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani Sarkin gargajiya kuma Obajisun na Masarautar Ayedun da ke Jihar Kwara mai suna Oba Dakta Olusegun Abayomi JP ya rasu a ranar Talata.
Abayomi ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Afr Babalola da ke Ado Ekiti a Jihar Ekiti bayan fama da wani gajeren rashin lafiya.
Marigayin, wanda ya yi bikin cika shekaru 85 a ranar 16 ga Mayu, 2026 ya shahara da nagartar jagoranci tun daga tushe kuma wanda ya samar da sauye-sauyen ci-gaba ga Masarautar Ayedun.
Haka kuma yana ɗaya daga cikin sarakuna 10 da Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya kara wa matsayi zuwa sarakuna masu daraja ta ɗaya.
