Daga AISHA ASAS
Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Kwalliya na jaridar Blueprint Manhaja. Sannunku da jimirin bibiyar mu.
Har yau dai muna kan darasin namu na ƙafa, inda a wannan makon da yardar Allah za mu tattauna kan matsalar fashewar diddige.
Masana lafiya sun bayyana cewa, fashewar diddige na daga cikin matsalolin da mutane da dama ke dauka da wasa duk da cewa tana iya rikiɗewa zuwa babbar matsala idan aka yi sakaci.
A cewar likitoci, bushewar fata, rashin shafa mata mai, yawan tafiya babu takalmi da kuma amfani da sabulai masu tsananin sinadarai na daga cikin abubuwan da ke haddasa matsalar.
Sun ce idan diddige ta fashe sosai har ya fara zubar jini, kwayoyin cuta na iya shiga cikin jiki ta wurin.
Likitan fata Dakta Maryam Idris ta bayyana cewa: “Mutane da yawa kan zo asibiti ne bayan matsalar ta tsananta. Alhali tun farko ana iya daƙile ta da sauƙin kulawa.”
Masana sun ba da shawarar amfani da mayuka masu tashi da tushi ga fata musamman waɗanda ke ɗauke da glycerin ko petroleum jelly.
Haka kuma sun ce shafa wa ƙafa mai kafin kwanciya tare da sanya safar kafa mai laushi na taimakawa wajen dawo da laushin diddige.
