Mutanen gari sun fatattaki ‘yan bindiga tare da kashe huɗu daga cikin su a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga da suka kai hari a ƙauyen Ɗansarai, da ke ƙaramar hukumar Malumfashi a Jihar Katsina, sun gamu da turjiya daga mazauna ƙauyen a ranar Talata.

Mazauna yankin sun shaida wa Daily Trust cewa maharan sun kutsa cikin ƙauyen ne a kan babura, ɗauke da muggan makamai ciki har da bindigogin AK-47.

Rahotanni sun ce maharan sun riƙa yin harbi kan mai uwa da wabi lamarin da ya yi sanadin mutuwar mazauna ƙauyen huɗu.

Wannan lamari ya harzuƙa mazauna ƙauyen inda suka yi kukan kura suka tunkari yan bindigar.

Wani mazaunin ƙauyen ya ce sun yi nasarar fatattakar ‘yan bindigar, inda suka kashe huɗu daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere daga yankin.

By ukarofi

Leave a Reply