Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ce wajibi ne Nijeriya ta yi duk mai yiwuwa domin kauce wa sake faɗawa yaƙin basasa, yana mai gargaɗin cewa ƙasar ba za ta iya jure wani irin rikici makamancin na 1967 zuwa 1970 ba.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a Abeokuta yayin ƙaddamar da wani littafi da Chuck Nduka-Eze ya rubuta kan kisan gillar Asaba da abubuwan da suka shafi yaƙin basasa.
Ya ce har yanzu wasu daga cikin matsalolin da suka haddasa yaƙin basasa suna nan, don haka dole ne a koyi darasi daga tarihi tare da tabbatar da cewa irin wannan bala’i bai sake faruwa ba.
Tsohon shugaban ya yaba wa marubucin saboda rubuta tarihin kisan gillar Asaba, yana mai cewa adana tarihi na taimakawa wajen warkar da raunukan da suka gabata da kuma ƙarfafa haɗin kan ƙasa.
Obasanjo ya kuma bayyana cewa duk da ya taka rawa a yaƙin basasa a matsayin kwamandan soja, ba shi ne ke jagorantar ayyukan soji a Asaba ba, inda ya ce Marigayi Janar Murtala Mohammed ne ke kula da yankin a lokacin. Ya ƙara da cewa daga baya an ba shi alhakin tabbatar da cewa ba a sake cin zarafin fararen hula ba, yana mai jaddada cewa rundunar soji ba ta amince da cin zarafin jama’a ba.
Ya kuma tuna cewa tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Yakubu Gowon, ya taɓa neman afuwa kan kura-kuran da aka aikata a lokacin yaƙin basasar Nijeriya.
