Kano na cike da ɗumbin tarihi — Rose Madaki

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Shugabar Hukumar Kula da Gidajen Tarihi da Kayan Tarihi ta ƙasa (National Commission for Museums and Monuments – NCMM), reshen Jihar Kano, Rose Madaki, ta bayyana cewa Jihar Kano na daga cikin jihohin Nijeriya da suka fi arzikin tarihi da al’adun gargajiya.

Ta bayyana hakan ne yayin wani taron wayar da kan jama’a kan muhimmancin adana tarihi da kayan tarihi, wanda aka gudanar a Gidan Tarihi na Makama da ke Kano a makon da ya gabata. Taron ya samu halartar manyan baƙi, ciki har da Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sunusi II.

A jawabinta, Rose Madaki ta ce Kano ta yi fice saboda dogon tarihinta na ƙarni da dama, wanda ya sa ta zama ɗaya daga cikin cibiyoyin tarihi mafi muhimmanci a Nijeriya da ma Afirka.

Ta ce katangar Kano da tsofaffin ƙofofinta, irin su ƙofar Nassarawa, ƙofar Famfo, Sabuwar ƙofa, ƙofar ɗan Agundi, ƙofar Na’isa, ƙofar Gadon ƙaya, ƙofar Kansakali, ƙofar Dukawuya, ƙofar Wambai, ƙofar Waika, ƙofar Mata, ƙofar Dawanau da ƙofar Ruwa, na daga cikin muhimman abubuwan tarihi da ke nuna martabar Kano.

Ta ƙara da cewa Gidan Tarihi na Makama na adana tarin kayan tarihi da ke jan hankalin masu bincike, ɗalibai, masu yawon buɗe ido da sauran baƙi daga sassa daban-daban na duniya.

Shi ma wani jami’in NCMM, Alhaji Ahmad, ya bayyana cewa Nijeriya ƙasa ce mai ɗimbin tarihi tun kafin bayyanar Annabi Isa (AS), yana mai cewa ƙasar na da muhimman al’adu da kayan tarihi da za su iya gogayya da na ƙasashe irin su Masar da Habasha.

Ya yi kira ga gwamnati da al’umma su ci gaba da kare kayan tarihi domin su kasance gadon al’ummomi masu zuwa.

By ukarofi

Leave a Reply