Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta fara sauraron ƙarar da Hon. Khamisu Ahmed Mailantarki ya shigar, inda yake ƙalubalantar takarar Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a Jihar Gombe.
Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed ce ke jagorantar shari’ar.
Mailantarki ya shigar da ƙarar ne a kan jam’iyyar PDP, Pantami da kuma Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), yana mai zargin cewa an zaɓi Pantami ta hanyar naɗi maimakon gudanar da zaɓen fidda gwani kamar yadda dokokin jam’iyyar suka tanada.
Ya kuma yi iƙirarin cewa jam’iyyar ba ta amince da wata yarjejeniyar maslaha da ta bai wa Pantami tikitin takara ba.
A cewarsa, Pantami ba ya cikin waɗanda suka nemi tikitin takarar gwamna a PDP, domin bai sayi fom ɗin takara ba, kuma bai halarci tantancewar ‘yan takara da jam’iyyar ta gudanar ba.
Mailantarki ya ƙara da cewa Pantami ya fara neman takarar gwamna ne a jam’iyyar APC, kuma a lokacin da aka ce an amince da tsarin maslaha a PDP, bai zama cikakken ɗan jam’iyyar ba.
Saboda haka, Mailantarki na roƙon kotu ta soke Pantami a matsayin ɗan takarar gwamnan PDP, tare da umartar a cire sunansa daga jerin ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar a Jihar Gombe.
A zaman kotun, lauyan INEC, Barista Ayuba Peter, ya ce hukumar ta samu umarnin kare kanta ne kwanan nan, saboda
