Bayern na shirin ninka albashin Michael Olise, zai kai daidai da na Kane

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich na ƙoƙarin ƙara wa wa’adin ɗan wasanta Michael Olise tsawo yayin da Real Madrid da PSG suke nuna kwaɗayi akansa.

Akan haka ne Munich ta fara shirin masa tayin sabon kwantaragi da zai kai wa’adin nasa zuwa Yunin 2031, wanda zai ɗaga albashinsa na shekara-shekara daga Yuro miliyan 12 zuwa kusan Yuro miliyan 25, lamarin da zai sa ya yi kankankan da ‘yan wasa Harry Kane da Jamal Musiala.

Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Olise ya yi gagarumin ƙoƙari wa Bayern a kakar wasa na 2025/26, inda ya zura ƙwallo 20 tare da bayar da 25 aka ci a ƙarƙashin koci Vincent Kompany, lamarin da ya sa ya zama ɗaya daga cikin masu neman samun kyautar Ballon d’Or.

Haka kuma, haskawar ɗan wasan ta sanya Faransa shiga gasar Kofin Duniya, wanda hakan ya sa ake raɗe-raɗin Real Madrid ka iya taya shi akan miliyan €150.

Saidai duk da haka, Shugaban Bayern, Herbert Hainer ya ce kwantaragin Olise yana nan har 2029 ba tare da yarjejeniyar sayar da shi ba, yana mai cewa ƙungiyar ba ta shirya wa hakan ba.

By Babaji

Leave a Reply