Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli ya shawarci iyaye da su dena ɓarnatar da kuɗi wajen yin kwalliya da anko da sauran bidi’o’in biki a lokacin aure.
Da ya ke jawabi a taron bikin cika wata ƙungiyar addini mai suna Crystal Muslim Organisation (CMO) a Abuja a ranar Asabar, Sarkin ya ce kamata ya yi a riƙa amfani da irin waɗannan kuɗaɗen wajen taimakon marasa ƙarfi da taimakon addini.
Sarki Bamalli ya kika cewa duk da irin matsin rayuwa da ake ciki, iyaye, musamman masu hannu da shuni na ci gaba da sharholiya da kudade a lokutan bukukuwa na tare da tausayin na ƙasa ba.
Sarkin ya lura cewa irin hakan ne ke haifar da matsaloli da rashin zaman lafiyAya tsakanin al’umma.
“Za ka ga mutanenmu su na kashe miliyoyin Naira kan kwalliya kawai idan za a yi bikin auren ‘ya. Wasu iyaye ma sun kai ga kashe har dala $10,000 wajen yin kwalliyar amarya. Ko kuma su sayi anko da kudin sa ya kai Naira dubu 500,000, Naira dubu 200,000 ko Naira dubu 300,000. A gani na, wannan ba daidai ba ne ko kaɗan.
“Akwai mutane da dama a kan tituna da ba sa iya samun abinci sau uku a rana. Don haka, wannan almubazzaranci ya yi ƙamari a cikin al’ummar mu. Amma wasu daga cikinmu mun ɗauki matsaya. Ni kam, ban taɓa kashe ko sisi ba wajen sayen anko ko biyan kuɗin kwalliyar yarinya da za ta yi aure ba. A’a. Idan mahaifiyarta ta zaɓi yin hakan, wannan ita ta ga dama. Ko kuma idan wani yana son yin hakan, ya yi, amma ni ba zan kashe ko sisi akan hakan ba.
“Su na kashe kuɗaɗe masu yawa a bukukuwa waɗanda a zahiri ba su da wani amfani. Ba ina cewa kada a yi biki ba ne, amma akwai abubuwan da ya kamata mu rage kashe kuɗi a kansu.
“Dole ne mu faɗawa kanmu gaskiya. A halin da ƙasar nan ke ciki a yanzu, ba mu da buƙatar irin waɗannan abubuwan na almubazzaranci,” in ji Sarkin.
Ya yi kira da a rage kashe kuɗi barkatai ba tare da taimakon marasa ƙarfi ba, inda ya ce hakan ka iya haifar da matsaloli cikin al’umma.
