
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Benuwai (SSG), Farfesa David Salifu, ya rasu bayan samun rauni daga harbin bindiga a wani hari da ‘yan bindiga suka ƙaddamar akan hanyar Wukari zuwa Zakibiam da ke tsakanin jihohin Benuwai da Taraba.
Rahotanni sun bayyana cewa, farfesan, wanda shi ne SSG a zamanin mulkin tsohon gwamna Gabriel Suswam, ya rasu ne a safiyar ranar Juma’a a lokacin da ake masa magani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Benuwai da ke Makurɗi bayan harin na ranar Alhamis.
Al’amarin ya auku ne a lokacin da marigayin ke kan hanyar tafiya daga Wukari a Jihar Taraba zuwa Makurɗi a safiyar ranar, inda wasu ‘yan bindiga suka tare motarsa a wajen garin Wukari.
Shaidu sun ce, maharan, waɗanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun tsayar da motar tasa ne, sannan suka umarci ya fito ya hawu kan babur. Saidai, ‘yan bindigar sun harbe shi a lokacin da yake ƙoƙarin ƙalubalantar su.
Farfesa Salifu tsohon lakcara ne a Jami’ar Tarayya da ke Wukari a Jihar Taraba.
Ɗan takarar kujerar sanatan Benuwai ta kudu a jam’iyyar ADC, David Olofu, wanda aboki ne ga marigayin, ya tabbatar wa manema labarai cewa Salifu ya rasu ne a safiyar Juma’a sakamakon raunukan jikinsa.
