Sojoji sun ceto hakimin Farin Hawa daga hunnun ‘yan bindiga a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

‎Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Fansan Yamma sun ceto hakimin Farin Hawa da ke ƙaramar hukumar Malumfashi a Jihar Katsina, bayan da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi.

‎A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 2 lokacin da maharan suka kai hari ƙauyen Farin Hawa inda suka sace hakimin, Alhaji Mubarak Sharin.

‎Rundunar ta ce bayan samun bayanan sirri, dakarunta tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun bi sahun maharan, inda suka yi musayar wuta da su.

‎A cewar sanarwar, an kashe ɗaya daga cikin maharan, yayin da sauran suka tsere, lamarin da ya bai wa dakarun damar kuɓutar da hakimin ba tare da ya samu rauni ba.

‎Har ila yau, rundunar ta ce a wani samame da aka kai tsakanin Amara da Chakau a ƙaramar hukumar Ɗanmusa, dakarun sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, jigidar harsashi ɗaya mai ɗauke da harsasai takwas da kuma babura guda biyu da ake zargin maharan na amfani da su.

‎Haka kuma, a wani artabu da aka yi a yankunan Sabon Gari da Dantakeri na ƙaramar hukumar Dutsinma, rundunar ta ce an kashe wani da ake zargin ɗan bindiga ne, yayin da wasu suka tsere.

‎Operation Fansan Yamma ta ce waɗannan hare-hare na daga cikin ci gaba da matakan da take ɗauka domin daƙile ayyukan ‘yan bindiga da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin Arewa maso Yamma.

By ukarofi

Leave a Reply