‘Suna sauya ma’anar kalamaina’: Akpabio ya faɗi dalilinsa na daina kallon talabijin

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya ce ya daina kallon talabijin ne saboda ana sauya ma’anonin kalamansa, yana mai cewa an jirkita ma’anonin kalamansa na kwanan nan akan ababen more rayuwa na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Akpabio ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin ƙaddamar da wasu titina a yankin Karsana da ke Abuja, inda ya bayyana cewa kalaman nasa sun taƙaitu ne kaɗai akan ayyukan da aka aiwatar a Abuja ba baki ɗaya ƙasar ba.

Ya ce, kalaman nasa na farko suna magana ne akan adadin ayyukan da aka ƙaddamar a birnin tarayyar daga Shugaba Tinubu da Ministan Abuja Nyesom Wike.

Ya ƙara da cewa, Wike ya sanar da shi cewa akwai sauran ayyukan da aka shirya ƙaddamarwa gabanin fara harkokin zaɓen 2027.

Kazalika, Shugaban Majalisar Dattawan ya ce akwai ayyuka da dama da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar a sassan ƙasar musamman akan ababen more rayuwa da suka haɗa da titin Badagry zuwa Sakkwato wanda ya akwai madatsar ruwa guda 74 ya rutsa ta cikinsu da ke bayar da gagarumar gudunmawa wajen cigaban harkokin noma a arewa.

By Babaji

Leave a Reply