Kofin Duniya: Moroko ta kai wasan dab da na kusa da na ƙarshe bayan lallasa Kanada

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙasar Moroko ta sake nuna bajintarta a gasar Kofin Duniya da ke gudana a Nahiyar Amurka bayan da ta lallasa ɗaya daga cikin masu masaukin baƙi, Kanada da ci 3 da 0 wasan zagayen ‘yan 16.

Ɗan wasan Atlas Lions, Azzedine Ounahi ya samu zura ƙwallo biyu a ragar Kanada, yayin sa Soufiane Rahimi da ya zo daga benci ya zura ta ukun ana gab da kammala wasan.

Haka ma Kyaftin, Achraf Hakimi da Brahim Diaz na Real Madrid, waɗanda sun taka rawar gani wajen kai farmaki inda suka bayar da ƙwallo biyun da Ounahi ya zura.

Wannan nasarar ta sa Moroko ta kafa sabon tarihi na zama ƙasar Afirka ta farko ta kasance a gasar Kofin Duniya cikin ƙasashe takwas da suka rage.

By Babaji

Leave a Reply