Daga AISHA ASAS
A wani mataki da ya ba da mamaki ga masoyansa, fitaccen jarumin fina-finan Nollywood Joseph Momodu ya sanar da cewa ya zama cikakken soja a rundunar sojin Amurka, bayan ya kammala horon farko na aikin soja cikin nasara.
Jarumin ya bayyana cewa wannan nasara ba kawai cikar wani buri na ƙuruciya ba ce, har ila yau hanya ce ta girmama mahaifinsa marigayi, wanda ya yi shekaru yana aiki a rundunar ‘yan sandan Najeriya.
Momodu ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, inda ya waiwayi tafiyar da ta kai shi ga shiga rundunar sojin, yana mai cewa watanni na sadaukarwa, horo mai tsauri da juriya ne suka ba shi damar kaiwa wannan matsayi.
Jarumin ya bayyana horon a matsayin ɗaya daga cikin mafi wahalar ƙalubalen da ya taɓa fuskanta a rayuwarsa, yana mai cewa an gwada ƙarfinsa na jiki, juriyar zuciyarsa da kuma azamarsa tun daga ranar farko har zuwa lokacin kammala shirin.
A cewarsa, akwai lokutan da ya fara tambayar kansa shin ko ya yanke shawarar da ta dace saboda tsananin wahalhalun da ake fuskanta yayin horon. Sai dai ya ce burinsa na cimma wannan mafarki ya hana shi yin kasa a gwiwa.
Ya ƙara da cewa horon ya canja rayuwarsa gaba ɗaya, inda ya koya masa muhimmancin ladabtarwa, haƙuri, haɗin kai da kuma jajircewa wajen fuskantar ƙalubale.
Momodu ya bayyana cewa ya zaɓi ranar 12 ga Afrilu, 2026 a matsayin ranar da zai cika burin shiga aikin soja domin tunawa da mahaifinsa, wanda ya rasu shekaru ashirin da suka gabata.
A cewarsa, shiga rundunar sojin Amurka wata hanya ce ta ci gaba da gadon hidimar ƙasa da mahaifinsa ya bari lokacin da yake aiki a rundunar ‘yan sandan Najeriya.
Ya ce ɗabi’un gaskiya, ladabi da sadaukarwa da mahaifinsa ya koya masa ne suka ƙarfafa masa guiwar ɗaukar wannan mataki.
Jarumin ya sanar da cewa ya yi nasarar kammala Basic Combat Training, lamarin da ya ba shi damar zama cikakken soja a rundunar sojin Amurka.
