Waɗanda ambaliyar Mokwa ta rutsa da su sun yi wa EFCC da ICPC ƙorafi kan zargin sauya akalar kuɗaɗen tallafi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu daga cikin mutanen da ambaliyar ruwa a Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja ta shafa, sun yi ƙorafi ga hukumomin EFCC, ICPC da kuma Rundunar ’Yan Sanda, inda suka buƙaci a gudanar da cikakken bincike akan yadda aka karba da kashe kuɗaɗe da kayan tallafin da aka tara domin taimaka musu.

Wannan mataki ya biyo bayan zarge-zargen da ake yi ne na karkatar da biliyoyin nairori da kayan agajin da aka ware domin tallafa wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a shekarar 2025.

Daga cikin ƙorafin da aka gabatar a ranar 26 ga Yuni, 2026, ta hannun ‘I.U. Wali Law Firm’, wasu mazauna Mokwa sun zargi wasu da cin hanci da rashawa tare da nuna rashin gaskiya wajen rabon kayan tallafi bayan mummunar ambaliyar ruwa da ta auku a yankunasu.

Masu korafin sun buƙaci hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da bincike mai zaman kansa domin tabbatar da gaskiya da kuma ɗaukar matakin da ya dace idan an samu waɗanda suka aikata ba daidai ba acikin al’amarin.

A tsakanin ranakun 28 da 29 da watan Mayun 2025 naka yi wata ambaliya mai ƙarfi ta lanƙwame kadarori ƙauyuka da dama na ƙaramar hukumar, lamarin da ya tilasta wa ‘yan yankin barin muhallansu.

By Babaji