Babban tarihi mafi kyau da Buhari ya bari shine zuba jari a fannin ilimi da gina al’umma

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Uwargidan tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta bayyana cewa babban abin a yaba da mijin nata ya rasu ya bari shi ne zuba jari a fannin ilimi da kuma gina al’ummar Najeriya.

A cewarta, Marigayi Buhari ya ba ilimi muhimmanci a lokacin mulkinsa, inda ya aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da suka yi niyyar inganta ilimi da bunƙasa damar samun ilimi ga ‘yan Najeriya.

Ta ce wannan ne zai ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan abubuwan da za a riƙa tunawa da shi a tarihin ƙasar nan.

A’isha Buhari ta bayyana haka ne a wajen ƙaddamar da tubalin fara ginin Tsangayar Nazarin Na’ura mai ƙwaƙwalwa, wato Faculty of Computing a jami’ar Al-Qalam ta Katsina, ranar Lahadi, 5 ga watan Yulin 2026.

Mai ɗakin tsohon shugaban ƙasar ta bayyana cewa, za a aiwatar da aikin ne da kuɗin da aka samu daga sayar da littafin ‘From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari.’

Da take jawabi ga manyan baƙi da suka halarci taron, A’isha Buhari ta ce aikin wata alama ce ta ƙudirin iyalan Buhari na ci gaba da raya tarihinsa.

By ukarofi