
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Asabar ne ‘yan bindiga sun halaka kimanin manoma guda tara da kuma yin awon-gaba da wasu da dama a wasu hare-haren gonaki da ke a bayan garin ƙauyen Kakangi a Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.
Rahotanni sun bayyana maharan sun buɗe wa manoman da ke aiki a gonakinsu wuta a lokacin da suka riske su suna bakin aiki, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum tara, kafin daga bisani suka tafi da wasu da ba a tantance adadinsu ba.
Al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3 na yamma yayin da manoman suke duba ababen da suka shuka.
Wani rahoton tsaro ya nuna cewa an gano gawarwaki tara zuwa yanzu, yayin da hukumomin yankin suka tabbatar da gano shida daga cikinsu.
Daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu akwai Habibu Danko, Zaharaddin Musa Gumu, Maibaka Mayana, Umar Maibaka, Yusufu Ɗankatakaki da kuma Shaf’iu Kagadama.
Sai dai wani jagoran al’umma a Birnin Gwari mai suna Kabiru Ishaq, ya ce mutum goma ne aka halaka.
A cewarsa, harin ramuwar gayya ne bayan wasu manoma sun yi yunƙurin kashe wani ɗan bindiga da ya yi ƙoƙarin kai musu hari, lamarin da ya sa ya koma ya dawo da ƙarin mayaƙa domin ɗaukar fansa.
Ƙananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Chikun da Kajuru da ke jihar na cigaba da fuskantar hare-haren ‘yan bindiga, inda ake yawan halaka mutane da garkuwa da wasu.
