Illar ta’addanci a cikin al’umma

Spread the love

Gwamnati ta fitar da jerin sunayen wasu mutane da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci. Abin takaici, da yawa daga cikin sunayen da aka bayyana suna daga cikin sunayen da aka fi sani a Musulunci da kuma Arewacin Nijeriya.

Muna addu’ar Allah Ya sa wannan ƙoƙari ya kasance na gaskiya wajen bankaɗo asirai da kuma hukunta duk wanda aka tabbatar yana da hannu a irin waɗannan munanan ayyuka. Babu abin da ke ƙara ta’azzara ta’addanci kamar rashin ɗaukar matakin shari’a da kuma gaza aiwatar da hukunci ga waɗanda aka samu da laifi.

Haƙiƙa, ta’addanci ba ya tsaya ga hare-haren ’yan bindiga ko masu tayar da ƙayar baya kacai. Akwai wasu munanan laifuka da su ma nau’in ta’addanci ne ga al’umma. Misali, lamarin marigayiya Ummulkhairi, wadda aka ce an miƙa ta hannun wasu fusatattun mutane, kuma aka danganta hakan da wani jami’in ’yan sanda mai mukamin DPO, lamarin da ya kai ga rasa rayuwarta. Haka kuma, akwai kisan wata mata da ’ya’yanta da aka yi a Jihar Kano, wanda shi ma babban laifi ne da ya girgiza al’umma.

Dukkan waɗannan munanan ayyuka ba ayyukan masu hankali ba ne. Don haka, fatarmu ita ce ba kawai a bayyana sunayen masu hannu a ta’addanci ba, har ma a gurfanar da su a gaban kotu, a gudanar da shari’a cikin adalci, sannan a aiwatar da hukuncin da doka ta tanada idan an same su da laifi. Yin hakan ne kaɗai zai zama darasi ga masu irin wannan mugun nufi, tare da taimakawa wajen rage aikata laifuka a cikin al’umma.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa, Katsina. 07066434519/08080140820.

By ukarofi

Leave a Reply