An samu fashewar bom a kusa da wajen taron da Emmanuel Macron ya halarta a Siriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu ababen fashewa guda biyu sun tarwatse a birnin Damascus, inda Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya halarci wani zama a ranar Talata yayin da ya kai ziyara Siriya.

A cewar Reuters, fashe-fashen sun faru ne a kusa da otal ɗin su Macron da ke babban birnin ƙasar, lamarin da ya tilasta wa hukumomin tsaro rufe hanyoyin zuwa yankin da ƙarfafa matakan tsaro.

An ruwaito cewa, boma-boman sun fashe ne a wajen taruwar jama’a da ke tsakanin ma’aikatar walwalar Siriya da gidan adana kayan tarihi a sassan yankin da Macron ya gana da ƙungiyoyin al’umma.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito cewa kimanin mutane 18 ne suka jikkata a sakamakon faruwar al’amarin ciki har da jami’an ‘yan sanda huɗu.

Haka kuma, an ga yadda hayaƙi ya ɗumama wajen, yayin da jami’an agajin gaggawa suka yi ƙoƙarin shawo kan al’amarin.

By Babaji

Leave a Reply