
A yau Talata Shugaba Bola Tinubu ya umarci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) da ta gudanar da cikakken bincike akan wata hukuma da ke kiran kanta Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC), wadda ta yi iƙirarin cewa tana ƙarƙashin Fadar Shugaban Ƙasa ne.
Umarnin ya biyo bayan gano cewa hukumar ba ta da wata doka ko sahalewar gwamnatin tarayya da ta kafa ta, kuma ba a taɓa amincewa da ita ta kowace hanya ba. Shugaban Ƙasar ya kuma ba ICPC wa’adin kwanaki 30 ta kammala binciken tare da miƙa masa cikakken rahoto.
A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, wani mutum mai suna Adeniyi Adeyemi Matthew ya riƙa gabatar da kansa a matsayin Darakta Janar na hukumar, tare da iƙirarin cewa shugaban ƙasa ne ya naɗa shi.
Ana kuma zarginsa da amfani da takardun naɗi na bogi da wasu takardun gwamnati na jabu wajen neman amincewar hukumomi da kuma tallafin diflomasiyya, ciki har da sauƙaƙa samun biza.
Baya ga haka, binciken zai kuma mayar da hankali kan zargin buɗe asusun bankuna da sunayen wasu hukumomin gwamnati ta amfani da takardun bogi, da gano yadda aka samar da waɗannan takardu, yadda aka yi amfani da su, da kuma tantance duk wani jami’in gwamnati, mutum ko hukuma da ka iya taimakawa ko sauƙaƙa aiwatar da zargin.
Shugaba Tinubu ya kuma umarci dukkan ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya su bai wa ICPC cikakken haɗin kai ta hanyar samar da bayanai da takardun da ake buƙata domin kammala binciken cikin gaggawa.
Ya jaddada cewa wajibi ne a kare mutuncin Fadar Shugaban Ƙasa da hukumomin gwamnati daga masu yin sojan gona, jabun takardu da amfani da sunan gwamnati ba bisa ƙa’ida ba, tare da umartar cewa duk wanda bincike ya kama da laifi ya fuskanci hukunci bisa tanadin doka.
