PSC ta kori manyan ‘yan sanda huɗu, ta rage wa 10 matsayi kan rashin ɗa’a

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da Harkokin ‘Yan Sanda PSC, ta amince da sallamar wasu manyan jami’ai guda huɗu bisa ayyuka da dama da suka shafi rashin ɗa’a, a wani mataki na horo da nufin ƙarfafa tsare gaskiya, adalci da ƙwarewa a Hukumar ‘Yan sandan Nijeriya.

Babban Jami’in Hulɗa da jama’ar PSC, Torty Njoku Kalu ne ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a ranar Talata, bayan kammala zaman manyan jami’an PSC a hedikwatarta da ke Abuja.

A cewar hukumar, an kuma rage wa wasu manyan jami’ai su 10 matsayi, yayin da aka ladabtar da wasu guda 31 duk dai akan ayyukan rashin ɗa’a.

PSC ta bayyana cewa, an samu huɗun da aka kora ne da hannu a laifukan rashin ɗa’a, nuna rashin ƙwarewa da ayyukan da ba su dace da kimar jami’an gwamnati ba.

Haka kuma, hukumar ta bayyana cewa, a jami’ai goman da aka rage wa muƙami har da Sufetocin ‘Yan Sanda (Superintendents of Police) uku da aka mayar da su Mataimakan Sufetocin ‘Yan Sanda (Deputy Superintendents of Police).

Sauran matakan da aka ɗauka sun haɗa da tilasta wa jami’ai biyu ritaya saboda maslahar al’umma, ba jami’ai goma takunkumi mai tsanani, gargaɗi ga jami’ai biyar, wasiƙar gargadi ga uku, da wasiƙar shawara ga jami’i ɗaya.

Bugu da ƙari, an wanke jami’ai guda bakwai daga zarge-zargen da ake musu na hannu a wasu laifuffuka.

Shugaban PSC, DIG Hashimu Salihu Argungu (mai ritaya), ya ce hukumar ba za ta lamunci duk wani nau’in rashin ɗa’a a rundunar ‘yan sandan ba, yana mai jaddada cewa hukumar za ta cigaba da hukunta masu laifi tare da ƙarfafa jami’an da ke aiki yadda ya dace.

By Babaji