An yi wa shugabancin ADC ƙorafin Sanata Nakudu kan zargin da ICPC ta yi masa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu mambobin jam’iyyar ADC reshen Ƙaramar Hukumar Gwaram a Jihar Jigawa, sun yi wa shugabancin jam’iyyar na Ƙasa ƙorafin Sanata Sabo Nakudu da ke neman takarar gwamnan jihar bisa iƙirarin rashin cika alƙawuran ayyukan mazaɓa Daga ɓangarensa.

Sun ce, Sanata Nakudu, wanda ya wakilci mazaɓar Jigawa ta Yamma daga shekarar 2015 zuwa 2023 na daga cikin waɗanda suka hana ruwa gudu a mazaɓar ta fuskar ayyukan ci-gaba da aka amince da aiwatar da su a hukumance.

A wata wasiƙa da suka aike wa Shugaban ADC na Ƙasa da ke ɗauke da sanya hannun Abubakar Sani da Ibrahim Mai Jama’a, sun ce wani rahoton Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ya nuna cewa an ƙwato dukiyar al’umma daga hannun Sanata Nakudu da wasu mutum biyu da adadinsu ya kai Naira biliyan 2.8.

Sun kuma ce, baya ga haka ICPC ta ƙwato motocin Hilux guda biyu, ɗaruruwan na’urorin famfon ruwa, babura da kuma injinan tono daga wasu kamfanonin Nakudu da wasu ‘yan uwansa biyu ke gudanarwa.

Akan haka ne suka yi kira ga shugabancin jam’iyyar da ya yi nazari akan hatsarin da ke tattare da tsayar da shi a matsayin ɗan takararta na gwamna a Jigawa a zaɓen 2027 da ke tafe.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da babban zaɓen 2027 ke cigaba da kusantowa, inda tawagar ke ganin tsayar da tsohon sanatan takara kuskure ne da ka iya janyo wa jam’iyyar faɗuwa bisa la’akari da rasa yardar al’umma akansa, kamar yadda suka yi iƙirari.

By Babaji