Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
ɗaya daga cikin jami’an kamfanin Albarka Poultry, Alhaji Umar Ibrahim, ya yi kira ga gwamnatocin tarayya da jihohi da su fara bai wa masu kiwon kaji tallafi kamar yadda ake yi wa manoma.
Ya bayyana hakan ne yayin wani taron wayar da kai da kamfanin ya shirya ga masu kiwon kaji a Kano domin bunƙasa sana’ar da inganta ribar masu gudanar da ita.
Alhaji Umar ya ce taron ya mayar da hankali ne kan koyar da dabarun zamani na kiwon kaji da hanyoyin samun riba mai yawa a sana’ar.
Ya kuma nuna damuwa kan yadda wasu kayan haɗa abincin kaji ba su sauko a farashi ba duk da raguwar farashin masara a kasuwa.
A nata jawabin, Hajiya Halima Abdullahi ta bayyana gamsuwarta da darussan da aka koya a taron, tana mai alƙawarin amfani da su wajen bunƙasa sana’arta.
Shi ma Sadisu Alƙasim, wanda aka fi sani da AA Bachirawa, ya bayyana matsalolin da masu kiwon kaji ke fuskanta, ciki har da rashin kasuwa mai kyau da kuma matsalar samun rance.
