Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Dan takarar gwamnan Jihar Kaduna na Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Rt. Hon. Isa Ashiru Kudan, ya ƙara zage damtse wajen gudanar da shawarwari da tattaunawar siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027, inda ya gana da tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, da kuma ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Hon. Mohammed Bello El-Rufai.
Ashiru ya gana da tsohon gwamnan ne a ranar Talata, kwanaki kaɗan bayan ya karɓi baƙuncin Bello El-Rufai a wata ziyarar ban girma.
Ya bayyana cewa jam’iyyar ADC ta shirya tsaf domin ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki tare da samar wa al’ummar Kaduna wata madaidaiciyar madadin shugabanci.
Rahotanni sun nuna cewa waɗannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da sauye-sauyen siyasa da ƙulla alaƙa tsakanin ‘yan siyasa a Kaduna da sauran sassan ƙasar nan gabanin zaɓen 2027.
Da yake wallafa bayan ganawar a shafinsa na Facebook da aka tabbatar nasa ne, Isa Ashiru ya bayyana tattaunawar da suka yi da Nasir El-Rufai a matsayin mai amfani da kuma wadda ta ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen tunkarar zaɓen gwamna na 2027.
Ko da yake bai bayyana inda aka gudanar da taron ba, majiyoyi sun ce an yi ganawar ne a Abuja.
A cewarsa, tattaunawar ta ƙara tabbatar da kudirin jam’iyyar na samar da shugabanci mai ma’ana wanda zai iya magance matsalolin da ke addabar Jihar Kaduna.
“Tattaunawarmu ta ƙara mana ƙwarin gwiwa. ADC a Kaduna ba kawai a shirye take ba ne, har ma tana da ƙarfin da za ta iya kawar da gwamnatin APC da ta gaza biyan bukatun al’ummar jihar,” inji Ashiru.
Ya zargi gwamnatin APC da gaza cika alkawuran da ta ɗauka wa al’ummar Kaduna, yana mai cewa jihar na buƙatar shugabanci da zai fifita adalci, ci gaba da kuma shugabanci mai haɗa kowa da kowa.
“Ya isa haka nan da wahalhalu da uzurori. Ta hanyar haɗin kai da jajircewa da kuma goyon bayan jama’a, za mu dawo da adalci, ci gaba da martabar Kaduna. Shekarar 2027 za ta kasance shekarar ceto ga jihar Kaduna,” inji shi.
Ganawar da Ashiru ya yi da Nasir El-Rufai ta zo ne sa’o’i kaɗan bayan ya gana da Hon. Mohammed Bello El-Rufai, ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Kaduna ta Arewa.
Bayan ganawar, Ashiru ya yaba wa ɗan majalisar bisa ayyukan raya mazabu da kuma abin da ya kira kyakkyawan wakilci a Majalisar Wakilai.
Ya ce Bello El-Rufai ya nuna cewa ana auna nasarar mai riƙe da muƙamin gwamnati ne da irin tasirin da ya yi ga rayuwar mutanen da yake wakilta.
A cewarsa, ayyukan da ɗan majalisar ya aiwatar sun amfanar da al’ummar Kaduna ta Arewa tare da nuna jajircewarsa wajen kyakkyawan wakilci.
Ashiru ya kuma yaba wa gudunmawar Bello El-Rufai a ɓangaren ayyukan majalisa, yana mai cewa shugabanci nagari yana ta’allaka ne a kan hidima da sakamako mai anfani ga jama’a.
Ya sake jaddada aniyarsa ta samar da shugabanci mai haɗa kowa da kowa, haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa idan aka zaɓe shi gwamnan jihar.
Masana harkokin siyasa na ganin cewa ganawar da Ashiru ya yi da Nasir El-Rufai da Bello El-Rufai na nuna yadda ake ƙoƙarin ƙarfafa haɗin gwiwa da tattara goyon baya tsakanin ɓangarorin adawa gabanin zaɓen 2027.
Ana kuma kallon wannan a matsayin wata alama ta sauye-sauyen siyasa da ke gudana a Jihar Kaduna, inda jam’iyyun siyasa ke ci gaba da gudanar da shawarwari da haɗa ƙarfi tun kafin fara yaƙin neman zaɓe a hukumance.
Nasir El-Rufai, wanda ya yi gwamnan Kaduna tsakanin shekarun 2015 zuwa 2023, na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin fitattun jiga-jigan siyasar jihar, yayin da Bello El-Rufai ke ci gaba da jan hankali sakamakon ayyukansa a Majalisar Wakilai.
Da saura ƙasa da shekaru biyu a gudanar da babban zaɓen 2027, jam’iyyun siyasa da ‘yan takara na ci gaba da gudanar da shawarwari da tattara goyon bayan jama’a a faɗin jihar domin tunkarar abin da masana ke ganin zai kasance ɗaya daga cikin zaɓukan gwamna mafi zafi a tarihin Kaduna.
