Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya cika shekara ɗaya da rasuwa

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

A yau 13 ga Yulin 2026 tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ke cika shekara ɗaya da rasuwa, Buhari ya rasu a ranar 13 ga Yulin 2025 bayan ya shafe shekaru yana jagorantar ƙasar a matsayin shugaban mulkin soja da kuma shugaban ƙasa na farar hula.

Buhari ya fara shugabancin Najeriya a matsayin shugaban mulkin soja daga shekarar 1983 zuwa 1985, kafin daga bisani ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2015, inda ya sake samun wa’adi na biyu a 2019.

Ya miƙa mulki ga magajinsa bayan kammala wa’adinsa a shekarar 2023.

Blueprint Manhaja ta rawaito cewa za a gudanar da taron addu’ar cika shekara ɗaya ga tsohon shugaban ƙasar, a yau Litinin kamar yadda tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban ƙasar kan harkokin yaɗa labarai, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata.

Bashir Ahmad ya ce za a gudanar da taron ne a ranar Litinin, 13 ga Yuli, domin girmama Buhari da irin gudunmawar da ya bai Wa Najeriya a yayin da ya ke raye.

By ukarofi