‘Yan sanda sun sami nasarar ceto mata biyu daga hannun ‘yan bindiga a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Rundunar ‘yan sanda a Katsina sun nasarar ceto mata biyu daga hannun ‘yan bindiga a ƙaramar hukumar Charanchi tare da daƙile yunƙurin satar dabbobi a ƙaramar hukumar Charanchi.

Kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanar, ofishin ‘yan sanda a Kankia suka sami labarin cewa ‘yan bindiga a kan baburan hawa ɗauke da muggan makamai sun Kai hari a matsugunin Jauga a ƙauyen Sabon Gida da ke Kankia.

Ya bayyana cewa nan take jami’an ‘yan sanda suka isa ƙauyen inda su kai ta ɗauki ba daɗi wanda dole ya tilastawa ‘yan bindigan suka gudu suna ɗauke da raunuka a jikin su.

DSP Sadiq Aliyu ya ce ‘yan sandan sun sami nasarar ceto Rukkaya Yahaya yar shekara 20 da Sahura Abdullahi yar shekara 22 ba tare da sun sami ko ƙwarzane ba.

Haka Kuma DSP Abubakar Sadiq ya sanar da cewa yan sandan sun sami nasara daƙile yunƙurin satar dabbobi a Majen Waya da ke ƙaramar hukumar Charanchi.

Kwamishinan ‘yan sanda CP Ali Umar Fage ya jinjinawa jami’an sa bisa yadda suka nuna ƙwarewa da jarumtaka wajen daƙile yunƙurin aikata ta’adanci a waɗannan yankuna,ya kuma tabbatar da cewa jami’an sa na yin duk abin da ya wajabta wajen tabbatar da tsaro a Jihar.

By ukarofi

Leave a Reply