
Sabbin alƙaluman da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta fitar sun nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki ta ragu kaɗan da kaso 15.91 a watan Yuni na shekarar 2026, idan aka kwatanta da kaso 15.93 da aka samu a watan Mayu.
Sai dai duk da wannan raguwar da aka samu, rahoton ya nuna cewa farashin kayan abinci ya ci gaba da ƙaruwa, lamarin da ke ci gaba da jefa iyalai da dama cikin matsin rayuwa.
Kayayyakin da aka fi samun ƙarin farashi sun haɗa da tumatir, barkono, nama, wake, garin rogo, ayaba da sauran kayan masarufi da al’umma ke amfani da su a kullum.
Masana tattalin arziki sun bayyana cewa raguwar hauhawar farashi ba ta nufin kayayyaki sun yi araha ba. A cewarsu, har yanzu ‘yan Najeriya da dama na fuskantar ƙalubalen tsadar rayuwa, musamman wajen sayen kayan abinci.
Al’umma na ci gaba da fatan gwamnati za ta ɗauki ƙarin matakan da za su taimaka wajen rage tsadar rayuwa da sauƙaƙa wa jama’a wahalhalun tattalin arziki.
Taskar Gaskiya Media za ta ci gaba da kawo muku sahihan labarai cikin gaggawa.
