Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya ƙaddamar da asibitin Remawa da ke ƙaramar hukumar Rimi, wanda mai shari’a ta babbar kotun tarayya, Justice Binta Remawa, ta gina.
Gwamnan ya bayyana ziyarar a matsayin tarihi, yana mai cewa shi ne gwamna na farko da ya kai ziyarar aiki a Remawa tun bayan kafuwar Jihar Katsina shekaru 39 da suka gabata.
Ya yaba wa Justice Binta Remawa bisa gina asibitin, gidajen ma’aikata da rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana, tare da sanar da cewa za a shigar da mazauna 1,000 daga Remawa, Yargwamna, ’Yartsamiya da ’Yarnabanye cikin shirin KTSCHMA.
Waɗanda za su amfana sun haɗa da mata masu juna biyu, yara ‘yan ƙasa da shekara biyar, tsofaffi da masu buƙata ta musamman.
Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta samar da magunguna, ma’aikatan lafiya da kula da asibitin. Haka kuma ya ce aikin titin Remawa zai fara kafin ƙarshen wannan shekara ko farkon shekara mai zuwa, sannan ya yi alƙawarin gyara masallacin Juma’a na garin da kuɗinsa.
A ɓangaren ilimi, ya umarci ma’aikatar ilimi ta faɗaɗa makarantar sakandaren al’umma ta Remawa tare da kammala ƙarin ajujuwa uku, sannan a ɗauki malamai masu takardar NCE daga yankin domin koyarwa a garuruwansu.
Justice Binta Remawa ta ce ta gina asibitin ne domin magance matsalar rashin lafiya da ruwa a yankin, yayin da kwamishinan lafiya ya bayyana cewa asibitin zai amfani Remawa da ƙauyukan da ke maƙwabtaka da ita.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta gyara cibiyoyin lafiya takwas a ƙaramar hukumar Rimi, ta samar musu da kayan aiki, gidajen ma’aikata, motar ɗaukar marasa lafiya ta babur uku, tare da ɗaukar sabbin ma’aikatan lafiya 30 domin inganta kiwon lafiya a matakin farko.
