
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kwamitin Amintattu na Ƙungiyar Taron Matasan Nijeriya (YAN), ya sanar da kafa kwamitin shirya babban taronta na ƙasa da za gudanar a nan gaba.
A sanarwar da kwamitin amintattun ya fitar a ranar Lahadi, ya ce an shirya kwamitin ne bisa la’akari da tabbatar da tsare gaskiya da adalci ga kowane ɓangaren ƙasa.
Akan haka ne ma aka zaɓo wakilai daga baki ɗaya shiyyoyi guda shiga na faɗin Nijeriya, domin su tsara yadda za a gudanar da taron ba tare da fuskantar wata babbar matsala ba.
Ga jaddawalin ‘yan kwamitin kamar yadda sanarwar ta fitar:
“Rt. Hon. Samuel Godstime Chukwubuikem – Chairman
*Rt. Hon. Comrades Shuaibu Sani – Secretary
- *Rt. Hon. Famuyibo Nathaniel Oluwasegun – Member
- Prince Mohammed Sani Hassan – Member
- *Amb. Muhammadu Bello Dabai – Member
- *Amb. Albert Ezenwata Nwangwu – Member
- *Amb. Henry Ejiroghene Oghwere – Member
- *Alh. Esinrogunjo Musbau – Member
- *Amb. Sen Adeyelu Oluwadamilare Samuel – Member
- *Amb. Charles Ezeaniekwe – Member
- *Rt. Hon. Habiba Umar Iliyasu – Member”
Ana sa ran kwamitin zai tabbatar da shirya jaddawalin ayyukan taron da yadda za a gudanar da su bisa tsarin dokar ƙungiyar kamar yadda aka saba yi a kowace shekara.
