Shehu Mujaddadi bai ƙwace ƙasar kowa ba

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Wallahi akwai takaici da ban mamaki wani ɗan kwangilar AIFOB ko na makiya Arewa wanda ba shi ma da alaka ta kusa ko nesa da Hausawa; ya rubuta wai Shehu Mujaddadi ya ƙwace ƙasar Hausa ko ya yaƙi wani Sarki da sauran shirmen makirci da sai a soshiyal midiya dandalin bulus na Bello Badum a ke gani.

In ka deɓe ƙasar Gobir inda shi ma Shehu ɗan yankin ne, ba wasu wajaje da ya taka da kafarsa. Allah cikin ikonsa da’awarsa ta kai nisan inda ƙafarsa ba ta taɓa takawa ba. Hatta Gobir ɗin ma Wallahi Sarki Yunfa ne ya yi yunƙurin kisan gilla ga Shehu, da hakan ya sa Shehu kare kansa. In ba haka ba ai Shehu karantarwa ne kawai ya sa a gaba.

MASOYA NE SU KA TAFI WAJEN SHEHU DON KARɓO TUTA

Mu ɗau misalai a gurguje Sarkin Katsina na farko lokacin tajdidin Shehu, shi ne Malam Ummarun Dallaje wanda a ka haifa a Dallaje daf da Katsina kuma asalin iyayensa daga masarautar Kanen-Bornu su ka taho inda tushensu ma Larabawa ne na masarautar Wadai a Chadi amma wannan yarfen na JIHADIN FULANI ya sa a ke cewa Sarkin Fulani na farko na Katsina.

Sarkin Kano na farko lokacin tajdidi Malam Sulaimanu ma a Kano a ka haife shi kuma zuriyarsu ta Mundubawa sun dade a Kano kuma kula da ilimi da tsoron Allah ya sa a ka naɗa shi sarautar Kano inda bai bar dukiya ba a lokacin da ya rasu a 1819 kuma bai ma ambaci wanda zai gaje shi ba don koyarwa ce a gabansa. Nan a ka samu gidan Dabo su ka shigo sarauta inda daga nan a ka samu laƙabin Kanon Dabo.

Malam Musa da ya zama Sarkin Zazzau na farko zamanin tajididi ma ɗan asalin Zazzau ne daga zuri’ar Mallawa kuma shi ya tashi ya tafi don mara baya ga aikin raya Musulunci na Shehu.

WAJE MA DA ƙASAR HAUSA

In mun duba Modibbo Bubayero ma mai Gombe ai bai taba rayuwa a Gombe ta yanzu ba kuma hasalima a yankin Adamawa a ka haife shi inda don ƙaunar tajdidi ya tafi wajen Shehu ya karɓo tuta. Hakanan Malam Yakubu na Bauchi ya karbo tuta kuma bai kwace ƙasar kowa ba. Shi ya kafa Bauchi kuma har yanzu zuriyarsa ke sarautar masarautar.

Duk mai ƙaunar tajdidi a lokacin Shehu na samun albarkar shehu. Gaskiyar abun da ya faru malamai ne masu ƙaunar tauhidi su ka samu labarin fitowar Shehu a farkon ƙarni na 19 inda su ka yi tattaki daga yankunansu, su ka kai ma sa mubaya’a su ka kuma dawo sassan da su ka ci gaba da koyarwa. Duk mai kaunar tajdidi kuma mai ilimin addinin Musulunci ko almajiri/ɗalibin ilimi ka iya samun addu’ar Shehu don ya tafi ya ci gaba da karantarwa. Shehu iya nan Gobir ya zauna kuma ya rasu a nan garinsa a Sokoto da nan ma asalin ƙasar Gobir ne kuma shi ma haifaffen Gobir ne gaba da baya. Don an haifi Shehu a yankin Gobir a 1754 ya kuma rasu a yankin Gobir a 1817 a ka kuma yi ma sa kabari a nan yankin kuma har yau ɗin nan a nan ya ke.

Dududu Shehu ya yi kimanin shekaru 63 ne a duniya. Duk surutun nan da a ke yi Shehu bai bar dukiya fiye da littattafan addini da ya wallafa don amfanin Musulmin duniya ba. Makiya Shehu na yin hakan ne don kiyayya ga Musulunci. Haƙiƙa da Turawa su ka zo don yada add!ninsu, ba su ci bulus ba don sun samu Shehu ya kafa TAUHIDI kyam don haka su ka je gefen Daula su ka gama tsula tsiyarsu su ka koma a 1960. Haba in da Yammawa sun shiga Arewa sun same ta saƙaƙa ai da yau wani labarin a ke yi. Matsafa, mushurkai da ‘yan daudu ba za su taba son Shehu ba. Ai yanzu kun fahimci dalilin.

A nan ya na da kyau mu sake bitar yadda Turawan mulkin mallaka su ka yaƙi Daular Sokoto har a ka gwabza yaƙi su ka yi sanadiyyar kisa ga Sultan Muhammad Attahiru.

Don tsananin kafurci, bayan kisan gilla ga sultan muhammad Attahiru, ‘yan mulkin mallaka sun datse kan sa, su ka dau hotunan gawar su ka rarraba ko ina a Arewacin Nijeriya don firgita mutane cewa sun gama da Daular

Gwamna Lugga ya shiga sokoto ya nada sabon Sultan Muhammad Attahiru II da zabge ikon matsayin Khalifan Daula zuwa Sultan din Sokoto

Turawan Burtaniya sun canja komai sun sheƙar da jini; amma wallahi sun kasa hana kalmar shahada!

Kimanin shekaru 57 Turawan mulkin mallaka su ka yi a Arewacin Nijeriya gabanin miƙa mulki ga ‘yan ƙasa a 1960. Sun cimma nasarori da dama ciki da yada harshen turanci, yada addinin Kirista, kawo barasar zamani da zuƙar taba sigari kamar kabusu, amma abu ɗaya tak ya gagaresu shi ne sauyawa musulmi addini zuwa akalla dai su zama ‘yan duniya hayaƙin taba, ya zama zuwa masallaci sai Jumma’a ko sallar idi, ya zama musulunci sai an dawo gida a rabon gado ko makwabtaka amma in an shiga gari a bi tafarkin Bature. Haka dai Turawa su ka tattara komatsensu su ka koma ba tare da cimma babban muradinsu ba. Wannan na yi wa makiya ciwo musamman gyauron wadanda su ka bari a baya baƙaƙen Turawa da zuri’arsu yanzu ke kwangilar yaki da musulunci ta hanyar ɗinka rigar ƙabilanci da zummar haddasa yaƙin basasar a yi ta, ta kare a Arewa.

Sultan na ƙarshe mai mulkin Daula wato Sultan na 12 Muhammad Attahiru ya jagoranci mabiyansa su ka fice daga Sokoto da zummar hijira zuwa Madina a kauli mai inganci. Sojojin ‘yan mulkin mallaka su ka bi shi Bormi a jihar Gombe ta yanzu, nan a ka gwabza yaƙi su ka kashe Sultan da fille kan sa kuma su ka dau hotuna su ka rarraba a Arewacin Nijeriya don nuna an murƙushe Daular Sokoto.  

Sojojin mulkin mallaka sun kashe kusan dukkan jama’ar da ke tare da Sultan Attahiru fiye da mutum 600 ciki da ‘ya’yan Sultan 2 da Limamin Sokoto, amma su ma sun rasa wasu sojojin ciki da kwamandansu Bature Manjo Francis Marsh da ma wasu Turawan da bayanai su ka ƙididdige da 16. A nan a ka bunne Sultan da sauran marigaya. Hakanan shi ma Manjo Francis. In dangin Sultan da dangin Marsh sun gamu a shekarun baya wajen ziyara a Bormi ba sa kula juna. Rahotanni sun tabbatar da Turawa sun dade ba su ziyarci Manjo Marsh ba don haka ciyawa ma ta kange kabarinsa. Ya kamata masoya ‘yan mulkin mallaka su je su nome gewayen kabarin Marsh. Bormi na tazarar kilomita 4 daga garin Bajoga da ke arewacin Gombe kuma kimanin kilomita 76 daga Gombe.

ɗaya daga ‘ya’yan Sultan, Muhammad Bello da a ka yi wa lakabi da Mai Wurno ya jagoranci sauran waɗanda su ka tsira daga kisan Turawa ya isa da su kasar Sudan su ka zauna a can. Har yanzu dangin masu hijirar na zaune a Sudan.

Darasin da ke cikin wannan tarihi shi ne da waɗanda su ka yi kisan da wadanda a ka kashe duk ba saura ko mutum ɗaya a raye duk sun koma gidan gaskiya. Sarkin Ingila ma na zamanin King Edward ɓII ya riga mu gidan gaskiya a fadar Buckingham a 1910. Sarki George ɓ da ya biyo baya ya riga mu gidan gaskiya a 1936. Sai Edward ɓIII wanda a dalilin nacin wani aure ya rasa sarauta a cikin shekarar da ya hau karaga 1936. Sai Sarki George ɓI wanda ya hau a 1936 ya riga mu gidan gaskiya a 1952 kuma shi ne mahaifin wacce a ka fi sani a sabon zamanin nan wato Sarauniya Elizabeth wacce ta riga mu gidan gaskiya a 2022 bayan mulkin shekaru 70. Mun san dai yanzu danta Sarki Charles ne ke mulkin fadar Buckingham. Ba mamaki in shi ma rai ya yi halinsa ɗansa Yariman Wales William ya hau karaga. Kaninsa Harry na samun caccaka don rashin auren cikakkiyar Baturiya don haka shi da matarsa Meghan su ka zakuda daga lamuran sarauta su ka koma Amurka da zama.

KAMMALAWA

Gaskiyar magana kowa ya zauna lafiya da juna a guji karbo kwangilar makiya don tabbas, duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ne ruwan zai doka. Farafagandar ƙabilanci da duk wani sakarci a yi watsi da shi. Wannan zamanin kowa na da ‘yanci a tsarin mulki ya yi addinin da ya ke so ya kuma nemi dukkan mukamin da ya ke so matukar ya cancanta; amma sam ba a ba wa ɗan ƙasa hurumin ƙulla makirci na tada fitina ba kuma duk wanda ya kullawa kasa makirci na iya fadawa komar hukuma don fuskantar hukunci kamar yanda ya faru ga madugun ‘yan awaren Biyafar na IPOB Nnamdi Kanu wanda alƙali James Omotosho ya yi wa sassauci daga hukuncin kisa zuwa daurin rai da rai.

Duk wanda bai ji bari ba ai ya ji hoho kuma ai masu azancin zance na cewa zama lafiya ya fi zama dan Sarki. Nijeriya dai kasa ce da ta ba wa kowa hurumin yin addininsa da zama inda ya ke so ba tare da ya tsangwami wani ko wani ya tsangwame shi ba.

By ukarofi