Daga ABDULLAHI MUHAMMAD A Katsina
Hukumar KASSAROTA ta jihar Katsina ta fitar da wasu sabbin umarni da ta ce an tsara su ne domin inganta gudanar da aiki da kuma kare haƙƙin al’umma.
A wata sanarwar da sakataren jihar na KASSAROTA, Malam Aminu Lawal Batsari ya fitar, an haramta wa jami’an hukumar yin aiki a kan hanya da sanda ko wani nau’in makami, tare da hana bin mutane da gudu domin kama su.
Sanarwar ta kuma ce kada a kama tsofaffi, masu ɗauke da ɗaliban makaranta, ma’aikatan da ke kan aikin agaji kamar na lafiya, ko kuma magidanci da ke tafiya tare da iyalansa, sai idan ana zarginsu da aikata wani babban laifi.
Haka kuma, hukumar ta ce ta dakatar da kama masu babura saboda lasisin tuki, tare da haramta karɓar tara ba bisa ƙa’ida ba.
Kazalika, ta yi gargaɗin cewa duk wanda ya ci mutuncin jami’an KASSAROTA zai fuskanci matakin hukunci.
Hukumar ta ƙara da cewa ƙofar ofishinta a buɗe take ga duk wanda ke da sahihin ƙorafi domin a saurare shi.
