
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya kai ziyarar girmamawa ta musamman ga tsohon gwamna kuma tsohon Sanatan Kano ta Kudu, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya a gidansa da ke Abuja.
Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya kai wa Sanata Kabiru Gaya, lamarin da ya ƙara nuna muhimmancin cigaba da tattaunawa, haɗin kai da ƙarfafa zumunci tsakanin manyan jagororin jam’iyyar.
Ana ganin wannan a matsayin tayi na masamman domin janyo ra’ayin tsohon sanatan ya sauya sheƙa zuwa APC.
Al’ummar Kano ta Kudu na cigaba da bayyana fatansu na ganin Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya cigaban da kasancewa tare da Jam’iyyar APC, domin ƙarfafa haɗin kai da kuma taimakawa wajen samun nasarar jam’iyyar a Jihar Kano da Nijeriya baki ɗaya.
