Jam’iyyar NDC a Zamfara ta yi Allah-wadai da harin ‘yan ta’adda a jihar

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Reshen jam’iyyar National Democratic Congress, NDC a Jihar Zamfara ta yi Allah-wadai da sabbin hare-haren ‘yan ta’adda da suka kai a ƙananan hukumomin Talata Mafara da Bungudu.

Jam’iyyar ta yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dauda Lawal su ɗauki matakan gaggawa domin kawo ƙarshen ayyukan ‘yan ta’adda a jihar.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi mai magana da yawun jam’iyyar, Alƙassim Mustapha Kayatawa ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce ta karɓi labarin hare-haren cikin alhini da bakin ciki.

A cewar NDC, ‘yan bindigar sun kashe manoma da dama a al’ummomin Sauna da Ruwan Gora da ke ƙaramar hukumar Talata Mafara.

Sanarwar ta bayyana waɗanda aka kashe a matsayin ‘yan ƙasa masu aiki tuƙuru da ‘yan ta’adda suka yi wa kisan gilla ba zato ba tsammani.

Ta ƙara da cewa wasu da dama sun ji rauni mai tsanani kuma yanzu haka suna samun magani.

NDC ta bayyana damuwar ta bisa ga yadda ‘yan ta’adda suka mamaye garin Bungudu shelkwatar ƙaramar hukumar Bungudu, suka yi garkuwa da shugaban ƙaramar hukumar mai ci.

“A yayin harin, maharan sun kuma kashe jami’an tsaron shugaban, ciki har da ‘yan sanda biyu da mambobin ‘yan banga biyu.”

“Muna ta’aziyya ga iyalai na waɗannan jaruman da suka sadaukar da rayukansu suna gudanar da aiki. ” in ji sanarwar.

NDC ta Jihar Zamfara, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Surajo Garba Maikatako, ta bayyana hare-haren a matsayin munanan ayyukan ta’addanci a ta’asa.

Ta ce ci gaba da asarar rayukan marasa laifi da kuma kai hari ga shugabanin al’umma da jami’an tsaro wata barazana ce mai tsanani ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin jihar.

Jam’iyyar ta yi kira kai tsaye ga gwamnatin tarayya da ta jihar da su daina dogaro da alƙawuran yaƙin neman zaɓe na 2023 kawai , su maida hankali wajen kare dukkanin alummar Jihar.

“Saboda haka muna kira ga gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal su ɗauki mataki na gaggawa domin kawo karshen matsalar tsaro a Jihar,” in ji Kayatawa.

“Yana da muhimmanci a lura cewa shugabannin biyu sun yi manyan alƙawura a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023 na yaƙi da rashin tsaro da kuma kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya. Alhakinsu na farko bisa kundin tsarin mulki shine tabbatar da tsaron ‘yan Jihar Zamfara.”

NDC ta buƙaci shugabannin biyu da su ɓullo da dabaru masu aiki da kuma masu ɗorewa da za su ruguje cibiyoyin ‘yan ta’adda tare da mayar da zaman lafiya cikin al’ummominmu.

By ukarofi

Leave a Reply