Hukumar Zaɓe ta ƙasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta sanar da cewa za ta gudanar da zaɓen gwaji gabanin babban zaɓen ƙasa. Wannan mataki ya haifar da muhawara, inda wasu ke ganin tamkar wata alama ce da za ta iya bayyana ko za a samu gaskiya da adalci a zaɓe ko akasin haka.
Akwai kuma masu nuna rashin amincewa da shugabancin shugaban INEC, bisa wasu kalaman da ake zargin ya taɓa furtawa tun kafin ya hau kan wannan muƙami. Wasu na fargabar cewa hakan na iya sa a yi duk mai yiwuwa wajen bai wa gwamnati mai ci goyon baya domin ta sake komawa kan mulki.
Sai dai ya kamata mu fahimci cewa magudin zaɓe ba abu ɗaya ba ne. Idan jama’a suka ƙi fitowa yin zaɓe, hakan ma na iya zama wata hanya da ake amfani da ita wajen samun damar tafka maguɗi.
Haka kuma, wakilan jam’iyyu a rumfunan zaɓe (Agents) suna da muhimmiyar rawa wajen kare sahihancin zaɓe. Saboda haka, ya kamata kowane ɗan takara ya zaɓi wakilai nagari, masu gaskiya da riƙon amana.
Ina kuma kira ga jam’iyyun adawa da su daina mayar da hankali kan sukar gwamnati kawai. Idan gwamnati ta yi abin kirki, ya dace a yaba mata. Rashin yin hakan na iya ba gwamnati damar ci gaba da tafiya ba tare da cikakken sa ido daga ‘yan adawa ba.
Ga magoya bayan jam’iyyu kuwa, mu tuna cewa siyasa ba hauka ba ce. Idan kana goyon bayan wani ɗan takara ko jam’iyya, ka tabbatar ka mallaki katin zaɓe domin ka kaɗa ƙuri’arka. Haka kuma, idan ba ka goyon bayan wani ɗan takara, mafita ita ce ka yi amfani da ƙuri’arka, ba rikici, zage-zage ko cin mutuncin juna ba.
A ƙarshe, idan muka yi sakaci, zaɓe zai gudana ne yadda wasu suka tsara. Kuma idan hakan ta faru, talaka ne zai ci gaba da ɗaukar wahala, alhali masu siyasa da dama, duk da bambancin jam’iyyunsu, suna da kyakkyawar alaƙa da juna kuma suna taimakekeniya idan buƙatar hakan ta taso.
Daga MUKHTAR IBRAHIM SAULAWA, Katsina.07066434519/08080140829.
