Sojoji sun ceto shugaban kwalejin tarayya bayan daƙile yunƙurin hare-haren garkuwa a Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun Sashe na 2 a ƙarƙashin Atisayen FANSAR YAMMA a Shiyyar Arewa maso Yamma, sun yi nasarar daƙile wasu hare-hare na yunƙurin garkuwa a Jihar Zamfara, inda suka ceto Shugaban makarantar Federal Polytechnic da ke Ƙauran Namoda, Dakta Aminu Yusuf, iyalansa da wasu fararen hula guda 21 a atisaye daban-daban.

Rundunar soji ta sanar da cewa an gudanar da atisayen ne a ranar Litinin, 27 ga watan Yuli, 2026, wanda ke nuna samun galaba da take yi a yaƙinta da ayyukan ta’addanci a sassan shiyyar.

A wata sanarwa da Jami’in yaɗa labaran FANSAR YAMMA, Laftanal Kanal Aliyu Ɗanja ya fitar, ya ce sojoji sun samu kiran gaggawa a safiyar ranar akan cewa wasu ‘yan bindiga sun afka gidan shugaban makarantar da ke Layin Tsohon Tasha a Ƙauran Namoda.

An ruwaito cewa, maharan sun halaka mai gadinsa, sun raunata wani mazauni da kuma yunƙurin sace Dakta Yusuf da iyalansa kana jami’an tsaro suka isa yankin.

Bayan ɗauki-ba-daɗi na ruwan alburusai tsakanin sojoji da maharan, an yi nasarar ceto su yayin da su kuma ‘yan bindigar suka tsere sakamakon fin ƙarfi da dakarun tsaron suka nuna musu.

Wannan al’amari ya yi sanadiyyar ceto daktan da iyalansa ba tare da sun jikkata ko wani rauni ya same su ba.

A wani ɓangare a ranar hallau, an yi wa sojoji masu sintiri da dare kiran gaggawa daga ‘yan ƙauyen Tungan Ɗorawa a yankin Barkeji, inda a nan ma ‘yan bindiga suka yi yunƙurin sace wasu fararen hula.

Yayin da aka yi ba-takashi tsakanin ɓangarorin biyu, maharan sun tsere daga yankin, lamarin da ya ba sojojin nasarar daƙile harin.

Kazalika, rundunar ta ce a ƙauyen ne wasu ‘yan bindiga suka yi ƙoƙarin sace wani sanannen attajiri mai suna Alhaji Azaria, yunƙurin da bai yi nasara ba sakamakon mayar da martani daga ɓangaren sojoji. A halin ne sojoji suka ceto wasu mutane 21 da aka sace a gidajen maƙota tare da alhajin.

Har ila yau, dakarun tsaron sun kama wani Falalu Yusuf mai kimanin shekaru 45 bisa zargin sa da aikin tsegumi ga ‘yan bindigar, wanda tuni aka miƙa shi ga ofishin hukumar da ta dace domin gudanar da bincike akansa.

A ƙarshe, shugabancin atisayen ya jaddada aniyarsu ta cigaba da ƙoƙarin daƙile ayyukan ta’addanci da ke addabar yankuna da dama a Jihar Zamfara da ma Arewa maso Yamma baki ɗaya tare da tabbatar da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.

By Babaji

Leave a Reply