Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sanar da ƙarin albashi ga jami’an rundunar sojojin Nijeriya nan ba da jimawa ba, a wani yunƙuri na gwamnatin tarayya na inganta walwala da jin daɗin sojoji.
Musa ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wani taron horaswa da tallafa wa matan sojoji da kuma zawarawan sojojin da suka rasu. Ya ce gwamnati na ci gaba da ɗaukar matakan da za su inganta rayuwar jami’an tsaro da iyalansu.
A cewarsa, gwamnati ta riga ta ƙara mafi ƙarancin albashin wasu jami’an sojoji daga N49,000 zuwa N100,000, kuma ana ci gaba da shirye-shiryen sake ƙara albashin domin ƙarfafa musu gwiwa wajen ci gaba da kare ƙasa.
Ministan ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ta fahimci irin sadaukarwar da sojoji ke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, don haka za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da za su inganta walwalarsu da ta iyalansu.
A nasa jawabin, Babban Daraktan Hukumar Bunƙasa ƙanana da Matsakaitan Masana’antu (SMEDAN), Charles Odii, ya ce an raba tallafin Naira miliyan 25 ga mata da zawarawan sojoji 500 domin tallafa musu wajen gudanar da ƙananan sana’o’i.
Ya ƙara da cewa tallafin na daga cikin asusun gwamnatin tarayya na Naira biliyan 200 da aka ware domin bunƙasa ƙananan sana’o’i, yana mai bayyana cewa waɗanda suka yi amfani da kuɗin yadda ya kamata za su iya samun ƙarin tallafi a gaba.
