
Rundunar ‘yan sanda a Jihar Kano, ta ce ta ceto wani yaro ɗan shekara tara mai Ubaiyu Muhammad Sammani bayan tsawon makonni huɗu da yin garkuwa da shi.
Haka kuma, rundunar ta kama mutum 10 da ake zargi da hannu a sace yaron, waɗanda suka haɗa da maza guda tara da mace ɗaya.
Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce masu garkuwar sun nemi a biya su dala 30,000 kafin su saki yaron, wanda ke zaune a unguwar Rimin Kebbe cikin ƙoshin lafiya.
Ya ce, jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane ne suka gudanar da atisayen pceton a ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, bayan tattara bayanan sirri na tsawon lokaci.
A cewarsa, an ceto yaron ne a ranar 31 ga watan Yuli a yankin Ƙarshen Kwalta da ke Rimin Kebbe a Ƙaramar Hukumar Ungogo.
An gano shi a bayan gidan wanda ake zargi, Abubakar Salihu, wanda aka fi sani da Sankolo, wanda ya tsere kuma har yanzu ba a kama shi ba.
’Yan sanda sun ce bincike ya nuna cewa mutanen da aka kama sun taka rawa daban-daban wajen sace yaron, ciki har da ɓoye shi, neman kuɗin fansa.
Daga bisani an kai yaron Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, domin duba lafiyarsa, inda likitoci suka tabbatar da cewa yana cikin ƙoshin lafiya.
Rundunar ta ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa jami’an Sashen Yaƙi da Garkuwa da Mutane bisa nasarar aikin, tare da tabbatar wa al’ummar jihar cewa rundunar za ta ci gaba da yaƙi da manyan laifuka.
Ya kuma buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa ’yan sanda bayanan da za su taimaka wajen yaƙi da laifuka, inda ya ba da tabbacin cewa za su kare sirrin duk wanda ya bayar da bayani.
