
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Cif Lekan Alabi, wanda shi ne Abese Olubadan na Masarautar Ibadan, ya rasu bayan shafe shekaru 76 a duniya.
Marigayi Alabi, wanda tsohon ɗan jarida kuma tsohon sakataren yaɗa labaran tsofaffin gwamnonin Jihar Oyo ne, ya rasu ne a safiyar yau Asabar.
Mai taimaka wa Sarkin Ibadan, Oba Rashidi Ladoja akan harkokin yaɗa labarai, Adeola Oloko ne ya sanar da labarin rasuwar a wata takarda da ya fitar a Ibadan, babban birnin Oyo.
Ya bayyana cewa, marigayin ya rasu ne a Legas kuma za a yi jana’izarsa a gobe Lahadi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
