
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Asabar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta fara wallafa bayanan ‘yan takarar da jam’iyyun siyasa suka miƙa mata domin shiga takara a babban zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.
Ta ce, matakin biyayya ne ga hukunce-hukuncen Dokar Zaɓe ta 2026. Haka kuma, ya yi daidai da jaddawali da tsare-tsaren zaɓen da ta fitar a kwanan nan daga takardun da ‘yan takarar kujerar shugaban ƙasa suka gabatar domin zaɓen, wanda za a gudanar a ranar 16 ga Junairu 2027.
A sanarwar da ta fitar a ranar Asabar, INEC ta ce ta wallafa bayanan ne a a Babban Ofishinta na Ƙasa da ke Abuja da kuma ofisoshin ƙananan hukumomi shida na faɗin babban birnin.
A cewarta, ta ɗauki wannan mataki ne da nufin tabbatar da gaskiya da adalci ga al’umma musamman wajen ba su damar tantance takardun da ‘yan takarar suka bayar domin neman kujera, wanda hakan zai taimaka wajen yanke hukunci akan waɗanda ya kamata a zaɓa.
Da take wakiltar Kwamishinan Zaɓe na Abuja yayin aikin wallafar, Sakatariyar Gudanarwa, Bimbo Oladunjoye ta bayyana cewa hakan ya dace da hukuncin sashe na 29(3) na Dokar Zaɓe ta 2026, wanda ke umartar hukumar akan wallafa bayanan kai-tsaye da takardun karatu da suka shafi ‘yan takarar a yankunan da suka tsaya takara.
Ta bayyana cewa, wallafar ta ƙunshi ‘yan takarar shugaban ƙasa da ‘yan takarar kujerun majalisar dokokin ƙasa da ke takara a Abuja, tana mai cewa an gudanar da baki ɗaya aikin a ƙananan hukumomi shida na birnin tarayyar don sauƙaƙe wa al’umma.
