An shiga jimami yayin da ‘yan fashi suka harbe ‘yar ajin ƙarshe ta Jami’ar Tarayya ta Lafia

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

‘Yan uwa da abokan arziƙi da al’ummar Jami’ar Tarayya da ke Lafia (FULAFIA) a Jihar Nasarawa, sun shiga alhini bayan wasu ‘yan fashi sun harbe wata ɗaliba ‘yar ajin ƙarshe mai suna Habiba Ummi Lele a jihar, lamarin da ke ƙara nuna ƙamarin halin tsaro da ke shafar ɗalibai a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa, an harbe Habiba ne a ranar Asabar a lokacin da ɓarayin suka buɗe wuta ga motar da ke ɗauke da ita a lokacin take kan hanyar koma wa Lafia bayan halartar bikin yaye wata ƙawarta da ta kammala karatu a Kwalejin Lafiya da Fasaha da ke Keffi. Ta rasu ne a nan take.

Shugaban Majalisar Zartarwar Ƙaramar Hukumar Awe, Hon. Umar Abubakar Ɗan’Akano da kuma ɗan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Awe ta Arewa, Hon. Hudu A. Hudu Kanje na daga cikin manyan mutanen da suka halarci jana’izarta, wanda aka gudanar a ranar Lahadi a gidan Hon, Kanje da ke Kanje.

Iyalai, abokai da jagororin al’umma sun haɗu don jajentawa a yayin jimamin rashin tare da gabatar da addu’o’i ga marigayiyar.

Abin tausayi da alhinin ya haddasa jimami a kafafen sada zumunta, inda ‘yan Nijeriya da dama suke bayyana jajensu da nuna damuwa kan taɓarɓarewar harkar tsaro a sassan Nijeriya.

Wannan al’amari na zuwa ne kwanaki kaɗan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka yi garkuwa da ‘yan aji ɗaya na jami’ar su uku a wani farmaki cikin dare da aka ƙaddamar a gidan kwanan ɗalibai na Sure Leaders da ke wajen farfajiyar makarantar a Bukan Kwato na Lafia.

By Babaji

Leave a Reply