Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar Hisba ta jihar Katsina ta umarci dukkanin jami’ai da kwamandoji na ƙananan hukumomi a kan su rika karɓo izinin kotu ko kuwa waranti, kafin shiga ɗakunan masaukan baƙi (hotels) ko kuma gidajen mutane don gudanar da aiki.
Umurnin dai na ƙunshe ne da rattaba hannun babban kwamandan hukumar, sannan kuma an cimma matsayar hakan ne a lokacin taron yau da kullum na hukumar da ya gudana.
A cikin wannan umurni dai, babu wani jami’i ko kwamanda da a ka amince ma wa ya shiga cikin wani masaukin baƙi ko gidajen mutane ba tare da samun izinin kotu ko kuwa waranti ba, sai dai ko in da dama dokokin da ake akwai sun amince da hakan.
Yin hakan dai na da nufin tabbatar da cewa, hukumar hisba na gudanar da ayyukan ta bisa tanaje-tanajen doka da kundin tsarin mulkin ƙasa da sauran dokoki da ke da alaƙa da ayyukan wajabta bin doka.
