‘Yan Kwara 176 da aka sace sun shaƙi iskar ‘yanci bayan watanni a hannun ‘yan bindiga

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kimanin mazauna sama da 176 na ƙauyen Woro da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara da aka sace ne suka shaƙi iskar ‘yanci bayan shafe watanni a hannun ‘yan bindigar da suka yi awon-gaba da su.

Mutanen, waɗanda aka yi garkuwa da su tun a watan Fabrairu yayin wani hari a ƙauyen, an ceto su ne a ranar Laraba a wani atisaye da ya haɗa jami’an hukumomin tsaro, lamarin da ya kawo ƙarshen halin rashin tabbas da iyalansu da ‘yan yankin suka shiga.

Wannan wata gagarumar nasara ce da aka samu a yaƙin da jami’an tsaro ke yi na ƙoƙarin kawo ƙarshen ayyukan garkuwa da mutane a jihar, inda tuni jami’an gwamnati da jagororin al’umma suka jinina wa ƙoƙarin hukumomin tsaro da suke da hannu a atisayen.

Ɗan majalisar dokokin jihar mai wakiltar mazaɓar Gweria/Bani/Adena, Hon. Saidu Baba Ahmed ya tabbatar da ci-gaban inda ya bayyana sako mutanen a matsayin abin farin ciki da zai sanya ‘yan ƙauyen numfasawa daga halin ƙuncin da suka tsinci kansu aciki a baya.

Ya bayyana godiyarsa ga Shugaba Bola Tinubu, Gwamna Abdulrahman AbdulRazaq da jami’an tsaro bisa ƙoƙarinsu wajen ganin an sako mutanen.

Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da Shugaban Ƙaramar Hukumar Kaiama, Hon. Abubakar Abdullahi Ɗanladi ya tabbatar wa mazauna yankin cewa ana ƙoƙarin ganin an ceto mutanen da aka sacen.

By Babaji

Leave a Reply