*Matakin da kotu da EFCC suka ɗauka gabanin zaɓe ya kunyata ni, cewarsa
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa, ba komai ake aikatawa a Gwamnatin Tarayya da shi shugaban yake da masaniya kafin yi ba. Don haka ya umarci Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) da ta garzaya kotu, domin janye umarnin da ya bai wa hukumar damar rufe asusun bankunan Gwamnatin Jihar Osun tare da dakatar da duk wani matakin shari’a da ta ɗauka kan lamarin.
A cikin wata sanarwa da Shugaban ƙasar ya sanya wa hannu da kansa mai ɗauke da kwanan watan 6 ga Agusta, 2026, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa abin da ya ba shi kunya ba shi ne yadda EFCC ta yi amfani da ikon da doka ta ba ta ba, sai dai lokacin da ta ɗauki matakin, kasancewar saura kwanaki kaɗan a gudanar da zaɓen gwamnan jihar.
Shugaban ƙasar ya ce, duk wani mataki da wata hukuma ta tarayya ta ɗauka, jama’a kan ɗauka cewa shi ne ya bayar da umarnin, ko da kuwa bai san da batun ba tun farko.
Ya ce, “An sanar da ni cewa EFCC ta samu umarnin kotu a ranar 5 ga Agustan 2026 na rufe da asusun Gwamnatin Jihar Osun. Abin da ya dame ni ba amfani da ikon da doka ta ba hukumar ba ne, sai dai lokacin da aka ɗauki matakin, domin duk abin da wata hukuma ta tarayya ta yi, mutane kan danganta shi da ni a matsayina na Shugaban ƙasa, ko da kuwa ban san da shi ba.”
Tinubu ya sake jaddada cewa tun bayan hawansa mulki ya kasance yana nacewa kan cewa hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran hukumomin tabbatar da doka su gudanar da aikinsu cikin ‘yanci, ƙwarewa da adalci, ba tare da tsoma bakin siyasa ko nuna son kai ba.
Ya bayyana cewa da gangan ya kauce wa ba EFCC ko wata hukuma mai bincike ko gurfanarwa umarni kan yadda za su gudanar da ayyukansu, saboda ya yi imanin cewa ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyya masu aiki cikin iyakokin doka na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da shugabanci nagari da bin doka.
“A matsayina na Shugaban ƙasa, na yi imani cewa hukumomin gwamnati su riƙa gudanar da ayyukansu da kansu ba tare da jiran amincewata ba. Wannan ne ma ya sa doka ta kafa su tare da bayyana musu ikon da suke da shi,” inji shi.
Sai dai shugaban ƙasar ya ce duk da cewa har yanzu bai samu cikakken bayani kan dalilan da suka sa EFCC ta nemi wannan umarnin kotu ba, yana da tabbacin cewa lokacin da aka ɗauki matakin bai dace ba.
Ya ce, “Ko da yake ban samu cikakken bayani kan abin da ya sa EFCC ta nemi wannan umarni ba, babu shakka a gare ni cewa lokacin da aka ɗauki matakin bai dace ba, kuma hakan ya sa na ga ya zama wajibi na sa baki.”
Tinubu ya bayyana cewa saura ’yan kwanaki kaɗan a gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Osun, saboda haka bai kamata a yi wani abu da zai sa mutane su yi zargin cewa ana amfani da EFCC ko wata hukuma ta gwamnatin tarayya wajen yin tasiri kan zaɓen ba.
A cewarsa, kare amincewar jama’a da sahihanci, gaskiya da adalcin tsarin dimokuraɗiyyar Nijeriya ne ya sa ya ɗauki wannan mataki.
