Zaɓen Osun: Davido da tsohon hadimin Buhari sun yi musayar yawu a kafar sadarwa ta zamani

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Fitaccen mawakin Nijeriya, David Adeleke da aka fisani da Davido da tsohon hadimin marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kan lamuran kafafen sada zumunta, Bashir Ahmad, sun tayar da hazo a Soshiyal Mediya inda suka yi musayar kalamai masu zafi a shafin X.

Wannan al’amari ya janyo hankalin jama’a musamman ganin yadda ba a saba ganin irin haka ba tsakanin mawaƙi ɗan kudu da ɗan siyasa daga arewacin Nijeriya.

Al’amarin ya samo asali ne a lokacin da aka ruwaito Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta sanya wa asusun gwamnatin Jihar Osun takunkumi gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a yi a ranar 15 ga Agusta, 2026, lamarin ya tayar da hazo da ɗaukar hankalin jama’a.

Bayan Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar kan tattaunawar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, Davido ya yi tsokaci.

A martaninsa, Davido ya rubuta cewa, “Ina wajen kai-tsaye (live)! Na shaida tarihi!!!”

Sai dai Bashir Ahmad ya mayar da martani, inda ya ce ya adana saƙon a matsayin hujja, yana mai cewa idan sakamakon zaɓen gwamnan Osun na ranar 15 ga Agusta bai tafi yadda Davido ke fata ba, zai dawo ya tunata da shi da rubutun nasa.

Akan haka ne Davido ya yi martanin cewa Bashir Ahmad ya samu ƙuri’u 16 kacal a zaɓen fidda gwani da ya taɓa shiga.

Daga lokacin ne Bashir Ahmad kuma ya ƙalubalanci Davido da tambayar yawan kyaututtukan Grammy da ya taɓa lashewa duk da yawan zaɓen da aka yi masa.

Davido ya bayyana cewa ba ya auna nasara da kyauta guda ɗaya, inda ya ce nasararsa tana cikin cika manyan filayen wasa, bidiyoyi, sauraron wakokinsa, tasirinsa a duniya da kuma yadda mutane ke rera wakokinsa a nahiyoyi daban-daban.

A ƙarshe, ya soki Bashir Ahmad da cewa duk da goyon bayan gwamnati, hakan bai samu isasshen goyon bayan jama’a a siyasa ba daga wajen jama’a.

Musayar kalaman ta cigaba da janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda magoya bayan ɓangarorin biyu ke bayyana ra’ayoyinsu kan al’amarin.

By Babaji

Leave a Reply