Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta sanar da kama mutum 48 da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci bayan wani samame na haɗin gwiwa da jami’an tsaro suka gudanar a sassa daban-daban na birnin Gusau.
Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce samamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da suka nuna wuraren da ake zargin maɓoyar ’yan ta’adda ne. Ya ce cikin waɗanda aka kama har da mata, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano irin rawar da kowannensu ya taka, inji shi.
Ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun kuma ƙwace babura 17, kekuna uku, janareta guda ɗaya, lasifika uku da ganguna uku, waɗanda ake zargin baragurbin ’yan ta’adda ne suka bari yayin da suka tsere daga wurin samamen, inji shi.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, CP A.M. Bello, ya jaddada ƙudirin rundunar na ci gaba da fatattakar masu aikata laifuka a faɗin jihar, tare da tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya kuma gargaɗi masu aikata miyagun laifuka da su daina ayyukansu ko kuma su fuskanci hukuncin doka, inji shi.
Rundunar ta ce samamen na daga cikin matakan da take ɗauka tare da sauran hukumomin tsaro domin ƙarfafa tsaro, dawo da zaman lafiya da kuma ƙara wa al’umma ƙwarin gwiwa a faɗin Jihar Zamfara.
